ABNA24 : Tun a ranar 27 ga watan Fabrairu ne dai ba a sake ganin shugaba Magufuli, ɗan shekaru 61 a duniya, a bainar jama’a ba sannan kuma ba a ji ɗuriyarsa ba lamarin da ya sanya aka fara raɗe-raɗin ya kamu da cutar COVID-19 ɗin.
Sai dai a jiya Juma’a, firayi ministan ƙasar Kassim Majaliwa cikin wani faifan bidiyo da aka naɗa yana cewa: Ina son in sanar da mutanen Tanzaniya cewa shugabansu yana nan cikin ƙoshin lafiya kuma yana ci gaba da ayyukansa sosai kamar yadda ya saba.
Sai dai kuma duk da wannan jawabi na firayi ministan wasu ‘yan ƙasar suna ci gaba da sanya alamun tambaya kan lafiyar shugaban suna masu cewa kamata yayi shi da kansa ya fito ya musanta wannan zargi da ake masa, kamar yadda babban jam’iyyar adawa ta ƙasar ita ma ta buƙaci shugaban da ya fito da kansa don yayi jawabi wa mutanen ƙasar.
Shugaba Magufuli ɗin dai yayi ƙaurin suna wajen musanta samuwar cutar ta COVID-19 da kuma ƙin amfani da magani ko kuma rigakafin cutar yana mai cewa ta hanyar addu’oi za a iya magance cutar.
342/